ABIN BUKATA Dankali guda 3 manya Man Suya (man gyada ko vegetable ko maka man cin su) Kwai guda 2 Filawa kadan Garin Tsidugu (Cayanne Pepper) Garin Kanunfari (Clove) Gishiri SHIRYAWA Da farko a fere dankali a wanke shi Sannan sai a kankare shi (grating) a cikin kwano (bowl) a zuba ruwa ya rufe shi A barshi a cikin ruwan tsawon miti 20 zuwa 30 … “Barin shi a cikin ruwa zai hana shi yin baki, kuma jikon zai sa shi yayi laushi” HADAWA Da farko sai a samu kwano a fasa kwan nan guda biyu a ciki A zuba masu Gishiri, garin Tsidugu (Cayanne Pepper) da garin Kanunfari (Clove) da ‘yar fulawa kadan a karkada. A dauko jikon dankalin nan a tsiyaye ruwan daga ciki kuma a matse ragowar ruwan jikin dankalin. Sai a dauko kawo hadin kwan da akayi a sama a zuba a ciki a kwaba. A samo kwanon suya (frying pan), a daura a kan wuta, a zuba masa mai (dai dai kamar na suyar kwai). Sai a kawon kwabin nan a zuba kadan kadan kanana. Idan gefe daya ya soyu sai a juya dayan gefen (kamar yadda ake suyar kwai).
0 Please Share a Your Opinion.:
Post a Comment