Amurka ta tsorata da harin korea ta arewa
Kasar Amurka ta razana da Yunkurin Kim Jong Shugaban kasa korea, na kai ma Kasar Amurka harin nukiliya,
Shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasar Amurka CIA,Mike Pompeo ya tabbatar wa duniya cewa,Amurka na bukatar tallafin dukannin kasashen duniya a wajen dakile yunkurin kai mata harin nukiliya da shugaban kasar Koriya ta Arewa,Kim Jong Un ya sa a gaba.
Amurka: “Ku agaza, Koriya ta Arewa na gaf da kai mana harin nukiliya”.
Shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasar Amurka CIA,Mike Pompeo ya tabbatar wa duniya cewa,Amurka na bukatar tallafin dukannin kasashen duniya a wajen dakile yunkurin kai mata harin nukiliya da shugaban kasar Koriya ta Arewa,Kim Jong Un ya sa a gaba.
Pompeo ya furta wadannan kalaman a yayin da yake jawabi a cibiyar nazari da kuma kare martabar mulki demokradiyya da ke a Washington, inda ya ce :
”Kamar yadda shugaban kasar Amurka,Donald Trump ya fadi a baya saura kiris Koriya ta Arewa ta fi karfinmu.Domin mataki guda daya ya mata saura, gabanin ta tanadi karfin illata kasarmu.Kuma ko shakka babu, za ta iya kai mana farmaki da makamin nukiliya a kowane lokaci. Shi yasa, loakci ya zo da ya kamata a ce, shugabannin duniya sun kawo mana dauki domin dakile yunkurin Kim Jong,
0 Please Share a Your Opinion.:
Post a Comment