Buhari Shugaban kasar Arewa ne kadai: injiinji Adebanjo
Arbawa Ya zargi shugaba Buhari A matsayin shugaban arewa Adebanjo ya ce duniya yanzu sun san shugaba Buhari na nuna kabilanci a mulkinsa.
Adebanjo ya zargi shugaba Buhari da kashe kudi a kan neman man fetur a yankin arewa Wani shugaban kungiyar ‘yan kabilar Yarbawa wato Afenifere, Ayo Adebanjo, ya tabbatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya nuna cewa shi shugaban arewa ne.
Majiyar Na ta tabbatar da cewar, Adebanjo ya yi wannan zargin ne yayin da yake mayar da martani a kan ikirarin da shugaban Bankin Duniya, Jim Yong Kim ya yi, cewa Buhari ya bukaci bankin ta fifita ayyukan ta a yankin arewacin kasar.
Da yake jawabi tare da jaridar Punch, Adebanjo ya ce yana da matukar damuwa cewa duniya yanzu sun san shugaba Buhari da nuna kabilanci a mulkinsa.
Adebanjo ya ce tun lokacin da shugaba Buhari ya shiga ofis dukan ayyukansa sun nuna cewa ba shi shugaban arewa ne kawai.
"Duk da kiraye-kiraye ta hanyar masana tattalin arziki, na cikin gida da na kasashen waje, cewa ya kamata Najeriya ta daidaita tattalin arzikinta
kuma ta rage dogara ga man fetur, amma Buhari ya ci gaba da kashe makudan kuɗi don binciken man fetur a yankin arewa , wannan alamun barnar kudi ne".
Duk abin da shugaba Buhari ya yi har yanzu tun lokacin da ya zama shugaban kasa ya nuna inda ya fito”, inji Adebanjo.
0 Please Share a Your Opinion.:
Post a Comment